Bisimillahir rahmir rahim, da sunan allah mai rahama mai jin kai.
Kamar yadda Allah (S.W.T) ya wajabta kaunar annabinsa a kan kowane musulmi. Hakama ya wajabta kaunar khalifofinsa akan ko wane mai imani. Idan mutum ya ga baya kaunar daya daga cikin khalifofinsa annabi (S.A.W), To ya tabbata bashi da imani.
Ga hadisai.
• An karbo daga Anas (R.T.A) (mar'fuan) daga annabi (S.A.W) cewa hakika shi ya ce. Lallai Allah ya wajabta kaunar Abubakar da Umar da Usman da Aliyu. Kamar yadda ya wajabta muku yin sallah da zakka da azumi da Hajji, wanda ya musanta fifikonsu (darajarsu) zo ba za a karbi sallarsa ba bare zakkarsa kuma ba za a karbi azuminsa ba bare hajjinsa. Dabari ne ya rawaito.
• An karbo daga Anas Allah yakara yadda a gare shi ya ce, kaunar Abubakar wajibice akan al'ummata.
• An karbo daga Aliyu dan Abi Dalibi (R.T.A) yace: hakika Allah mabuwayi da daukaka ya wajabta muku kaunar Abubakar da Umar da Usman da Aliyu. Kamar yadda ya wajabta muku sallah da zakka da azumi da hajji, Wanda ya yi gaba daya daga ciki (ya ki shi) to ba za a karbi sallarsa ba ko zakkarsa ko azuminsa ko hajjinsa. Kuma za a tashe shi a cikin kabarinsa izuwa wuta.
• An karbo daga Abdullahi dan Magafalin shi kuma daga annabi (S.A.W) hakika nace na hadu ko da Allah akan Sahabbaina ka da ku rike su karanbara a bayana, wanda ya so su to saboda kaunata ya so su, wanda kuma yaki so saboda yana kina ya ki su, Wanda ya cuce su to hakika ya cuce ni, Wanda ya cuce ni to Allah kuma Wanda kuwa ya cuci Allah to ya kusanta ya kama shi.
(Tabbihul gafilina)
• Abu hurairata ya rawaito Annabi (S.A.W) yace hakika kaunar wadannan guda hudu ba ta haduwa sai a zuciya mai imani, yana nufin Abubakar da Umar da Usman da Aliyu. Allah ya kara yadda a garesu.
• An karbo daga Aliyu (R.T.A) ya ce. Naji manzon Allah (S.A.W) ya ce hakika ubangiji madaukakin sarki ya umarce ni da na riki Abubakar (a matsayin uba) Umar kuma mai yimin ishara, Usman kuma madogara, Aliyu kuma mataimaki wadannan guda hudun allah ya riki alkawarinsu a cikin littafi, babu wanda zai kaunace su sai mumini mai tsoran Allah, kuma babu Wanda zai ki su sai fasiki shakiyi. Sune khalifofin annabtata ma'adanan hikimata kada Ku yanyanke kada ku rarraba.
• An karbo daga Abu huraira (R.T.A) yace mun kasance zaune tare da annabi (S.A.W) sai ga Abubakar Assiddiq (R.T.A) ya fuskanto sai manzon Allah (S.A.W) yace maraba da wanda ya taimake ni da dukiyarsa. Maraba da wanda ya zabe ni akan-kansa, Sannan Umar dan Khadabi (R.T.A) ya fuskanto, sai yace barka da mai rabewa a tsakanin karya da gaskiya madalla da Wanda Allah ya cika addini da shi kuma ya daga musulinci. Sai Usman Zunnuraini (R.T.A) ya fuskanto sai yace marhaban da surukina mijin 'ya'yana guda biyu Wanda Allah ya tara masa hasken arziki a rayuwarsa shahidi a ya yin mutuwarsa. Azabar wuta ta tabbata ga wanda ya kashe shi. Sannan sai ga Aliyu dan Abi Dalibi ya fuskanto sai yace maraba da dan uwana dan ammina, wanda aka halicce ni da shi daga haske guda daga. Ya ku taron musulmai kun ga wadannan kaunar su ba za ta hadu ba sai a zuciyar mai imani. Kuma ba za ta rabu ba sai a zuciyar munafiki wanda yake kaunar su Allah zai so shi Wanda kuwa yake kinsu to shima Allah zai ki shi.
thanks for share
ReplyDeletePost a Comment