Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Amma Abubakar Assiddiq Allah ya kara yadda a gare shi, shi ne farkon wanda ya bada gaskiya ga annabi Muhammad (SAW) a cikin mazaje. Kuma shine mafi soyuwa a wurin manzon Allah (SAW) hadisai sunyi cikakken bayani a kan matsayin Abubakar Assiddiq kamar haka:-
1) An karbo daga Abu Huraira (RTA) yace manzon Allah (SAW) yace babu wani wanda yake da hannu akan mu face hakika sai mun saka masa, amma banda Abubakar domin kuwa hakika shine ka dai yake da hannu akan mu wanda Allah ne kadai zai saka masa da ita ranar alkiyama. Dukiyar wani mutum ba ta ta ba amfana ta ba da dai kamar yadda dukiyar Abubakar ta amfane ni, da dai zan riki wani (mutum) badadi da na rika Abubakar badadi, sai dai cewa abokin nan naku badadin Allah ne.
(Tirmizi ne ya rawaito)
2) An karbo daga A'isha (RTA) ta ce Umar dan Khadabi ya ce. Abubakar shi ne shugabanmu kuma shi ne mafi alkairinmu. Kuma shi ne mafi soyuwar mu a wajen manzon Allah (SAW).
(Tirmizi ne ya rawaito)
3) An karbo daga Abdullahi dan Shakkin ya ce, na ce da A'isha wane sahabbi ne ya fi soyuwa a gurin manzon Allah (SAW) a cikin sahabbansa?, sai ta ce Abubakar. sai na ce sai kuma wa? sai ta ce umar. Sai na ce sai kuma wa? Sai ta ce sai Abu Ubaidata Ibn Jurahin. Sai na ce sannan kuma wa? Sai ta yi shiru.
(Tirmizi ne ya rawaito)
4) An karbo daga dan abbas, ya ce wata mata ta zo izuwa annabi (SAW) domin ta tambayeshi wani abu. Sai ya ce da ita to kije sai kin sake komowa, sai ta ce ya manzon Allah idan na dawo ban same ka ba fa, kana bujura da mutuwa? Sai ya ce idan kika dawo baki same ni ba to ki je wajan Abubakar domin shi ne khalifa a baya ba.
5) An karbo daga dan Abbas (RTA), ya ce manzon Allah (SAW) ya ce, ba a samu wani mafi girma a waje na kamar Abubakar ba, ya taimake ni da kansa da dukiyarsa kuma ya auramin 'yarsa.
Manzon Allah (SAW) ya ce, Abubakar shi ne fiyayyen wannan al'ummar sai dai in ya kasance annabi ne.
6) An karbo daga Abu Dardari ya ce (wata rana) Annabi ya ganni ina tafiya a gaban Abubakar, sai ya ce ya Abi Dardari yanzu kai ne ka ke tafiya a gaban wanda yake mafi alkairi a kan ka a duniya ko a lahira. Rana ba ta fito ta fadi akan wani mutum da yafi Abubakar ba in dai ba Annabi ba ne ko manzo ba.
7) An karbo daga A'isha (RTA) ta ce Abubakar ya zowa manzon Allah (SAW) sai ya ce (da shi) kai ne (Atiku) yantaccen Allah daga barin shiga wuta, daga wannan lokacin a cigaba da kiransa Atiku, yantaccen.
(Tirmizi ne ya rawaito)
8) An karbo daga A'isha (RTA) daga annabi (SAW) ya ce, bai da ce ba mutane akwai Abubakar a cikinsu a ce kuma waninsu ya shugaban ce su.
(Tirmizi ne ya rawaito)

Post a Comment