Da sunan Allah mai rahama mai kai.
Umar dan kaddabi shi ne khalifan mazon allah (SAW) na biyu, bayan Abubakar, musulinci ya sami daukaka daga ranar da Umar ya musulinta a cikin kasar makka. Saboda haka me mazon allah (SAW) ya ambace shi da faruku (mai rarrabewa tsakanin gaskiya da karya). Hadisai sun yi furuci kan matsayin Umar dan Khadabi (RTA) kamar haka:-
An karbo daga dan Umar (RTA) cewa hakika manzon Allah (SAW) ya ce ya Ubangiji na roke ka ka daukaka musulinci da mafi soyuwar mazajen nan guda biyu a wajenka, Abu Jahal ko Umar dan Khadabi. Sai ya ce mafi soyuwarsu a wajensa (shine Umar).
(Tirmizi ne ya rawaito)
Wannan addu'a ta manzon Allah (SAW) itace ta fada kan Umar dan Khadabi (RTA) har dai ya zo ya zama abin alfahari a cikin addinin musulinci.
An karbo daga dan Umar (RTA) manzon Allah (SAW) ya ce, lallai hakika Allah ya sanya gaskiya akan harshen Umar da zuciyarsa.
(Tirmizi ne ya rawaito)
An karbo daga Jabiru dan Abdullahi (RTA) ya ce (wata rana) Umar ya ce da Abubakar ya kai fiyayyen mutane bayan manzon Allah (SAW) sai shi kuma Abubakar ya ce, to amma idan kai ka fadi haka to hakika ni naji manzon Allah (SAW) yana cewa rana bata bullo akan wani mutum ba mafi alkairi daga Umar.
(Tirmizi ne ya rawaito)
An karbo daga Ukubatu dan Amrin ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, da dai wani Annabi zai kasance a bayana da ya kasance Umaru dan Khadabi.
(Tirmizi ne ya rawaito)
An karbo daga Abu huraira (RTA) ya ce Annabi (SAW) ya ce, Hakika ya kasance a gabanku bani Isra'ila mazaje da suke yin magana (akan wani abu kafin ya ksance) tare da cewa su ba Annabawa ne ba, to idan akwai irinsu a cikin al'ummata to Umar yana cikin su.
(Bukhari da Muslim da tirmizi ne suka rawaito)
An karbo daga dan Umar (RTA) wani al'amiri ba zai taba sakkowa mutane ba su yi magana akan abin shi kuma Umar ya yi magana akan face sai alkur'ani ya sauka abisa yadda Umar ya fada.
An karbo daga Abi Burdata (RTA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya wayi gari sai ya Kirawo Bilalu ya ce Bilalu ka rigaye ni izuwa Aljanna, ba zan shiga Aljanna ba da dai, face sai naji takun tafiyar ka a gaba na, a daran jiya na shiga Aljanna sai naji takun tafiyar ka a gaba, sai na zowa wani bene mai kusurwa hudu madaukaki na daga azurfa sai na ce wannan benan na wane? Sai suka ce na wani mutum ne daga cikin larabawa sai na ce ai nima balarabe ne, wannan benan na wane? Sai suka ce na wani mutum ne daga kuraishawa, sai ya ce ni ma bakuraishe ne, wannan benan na wane? Sai suka ce na wani mutum ne daga ummatu Muhammadu sai nace ai nine Muhammadun, wannan benan na wanene? Sai suka ce na Umar dan Khadabi ne, sai Bilalu ya ce ya Manzon Allah ban taba yin kiran sallah ba tunda nake face sai na yi sallah raka'a biyu, kuma babu wani wani abu da zai faru a gare ni face sai nayi alwala a wannan zamanin, kuma sai na ga cewa hakika Allah yana da raka'a guda biyu a kai na, sai Manzo Allah (SAW) ya ce to da wadannan guda biyun ne, (wato alwala da yin sallah raka'a biyu bayan kiran sallah ko afkuwar wani abu).
(Tirmizi da Bukhari da Muslim ne suka rawaito)
Post a Comment