Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.


Manzon Allah (SAW) ya yi wa Abubakar da Umar da Usamanu da Aliyu (RTA) bushara da gidan Aljanna, kamar yadda hadisai suka tabbatar. 


An karbo daga Abu Huraira (RTA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce, amma ka ganka ya Abubakar kai ne farkon wanda zai shiga Aljanna daga cikin al'ummata. (Abu Dauda)



An karbo daga Anas (RTA) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce da Abubakar da Umar, wadannan guda biyun sune shugabani gwarazan 'yan Aljanna na daga mutanan farkon da na karshe in banda Annabawa da Manzanni, kada ka basu labari ya Aliyu.

             (Tirmizi ne ya rawaito)



An karbo daga Anas (RTA) ya ce, Hakika Manzon Allah (SAW) ya ce, na shiga Aljanna, sai gani ga wani bene na daga azurfa, sai na ce wannan benan na wane? Sai suka ce na wani saurayi ne daga cikin kuraishawa. Sai na za ci nawa ne shi, sai na ce wanene shi? Sai suka ce Umar dan Khadabi. 

              (Tirmizi ne ya rawaito)



An karbo daga Abu Musa (RTA) ya ce na kasance a tare da Annabi (SAW) a cikin wani shinge mutanen madina. Sai wani mutum ya nemi a bude kofa, sai Annabi (SAW) ya ce bude masa kayi masa bushara da gidan Aljanna, sai na bude masa sai naga Abubakar ne, sai nayi masa bushara da abin da Annabi (SAW) ya fada, sai ya godewa Allah, Sannan sai wani mutum ya nemi a bude masa, sai Annabi (SAW) ya ce bude masa kayi masa bushara da gidan Aljanna, sai na bude sai naga ashe Umar ne sai nayi masa bushara da abin da Annabi (SAW) ya fada, sai ya godewa Allah, sa wani mutumin ya nemi a bude masa, sai Annabi (SAW) ya ce bude masa kayi masa bushara da gidan Aljanna a bisa wani bala'i da zai same shi, sai na bude sai naga ashe Usmanu ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post