Da sunan allah mai rahama mai jin kai.


Khalifofin annabi (SAW) sun kasance mutane masu tawaru'u a tsakanin su tare da daukakar allah (SWT) ya basu amma basa yi wa junansu girman kai, kuma ko wane dayansu baya ganin cewa ya fi dan'uwansa, kamar yadda ya zo a cikin hadisai kamar haka:

An rawaito cewa wata rana Umar da Usman, allah ya kara yadda a gare su, sunn kasance cikin wani aiki da Annabi (SAW) ya sa su, sai sallar La'asar ta same su, sai Umar dan Khadabi ya ce da Usman shige kayi mana sallah. Sai Usman ya ce kai ya fi dacewa dani akan shigewa ya Umar. Domin kuwa hakika manzon Allah (SAW) ya gabatar da kai kuma ya yi yabo a gare ka. Sai Umar ya ce ni kuwa ba zan shige gaban ka ba.  Domin kuwa na ji Manzon Allah yana cewa madalla da namiji Usmanu surukina mujin 'ya'yana biyu  Wanda Allah ya hada masa na guda biyu, sai Usman ya ce ni ma ba zan shige gaban ka ba domin kuwa na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa da Umar Allah ya kammala addini, sai Umar ya ce nima ba zan shige gaban ka ba domin kuwa naji Manzon Allah (SAW) yana cewa Mala'iku suna jin kunyar Usmanu, sai Usman ya ce, ni ma ba zan shige gaban ka ba domin kuwa Manzon allah  (SAW) yana cewa da Umar ne Allah ya cika addini kuma ya daukaka musulinci, sai Umar ya ce ni ma ba zan shige gaban ka ba domin naji Manzon Allah  (SAW) yana cewa Usmanu shi ne mai tattara Alqur'ani kuma masoyin Ubangiji arrahamani. Sai Usmanu ya ce ni ma ba zan shige gaban ka ba domin kuwa naji Manzon Allah (SAW) yana cewa madalla da namiji Umar wanda zai dinga nemi inda zawarawa suke da marayu ya dinga daukar abinci alhali suna barci yaje ya kai musu. Sai Umar ya ce ni ma ba zan shige gaban ka ba domin kuwa na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinka Allah ka yi fafata ga Usmanu wanda ya dauki nauyin mayakan tsanani (Tabuka). Sai Usmanu ya ce ni ma ba zan shige gaban ka ba domin kuwa na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinka. Allah ka daukaka musulinci da Umar dan Khadabi, kuma Manzon Allah (SAW) ya ambace ka da faruku. Ubangiji ya taba tsakanin karya da gaskiya da kai.

Sai labarin wannan al'ummar ya jewa Manzon Allah (SAW) na daga kyakkyawan ladabi a junansu sai ya sa aka kira su ya yi musu godiya, saboda ladabin da suka yi a junansu.







Post a Comment

Previous Post Next Post