Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Abu Huraira (RTA) ya ce hakika Abubakar Assidiku (RTA) da Aliyu dan Abi Dalibi sun gabato izuwa kofar gidan Annabi (SAW) sai Aliyu ya ce da Abubakar ka gabata domin ka zama kai ne farkon mai kwankwaso kofar da zai fara kwankwasawa, yana ce akan haka, sai Abubakar ya ce kai ne zaka fara gabata ya Aliyu. Sai Aliyu (RTA) ya ce ba zai yiwa na shige gaba mutumin da na ji Manzon Allah yana fada a cikin hakkinsa ba, cewa rana ba ta bullo ba kuma ba ta fadi ba a bayyana akan wani mutum da yafi Abubakar Assidiku. Sai Abubakar (RTA) ya ce ni ma kuma ba zan shige gaban wanda na ji Manzon Allah (SAW) ya na fada akan hakkinsa ba, na bayar da fiyayyar mace ga fiyayyen mazaje. Sai Aliyu (RTA) ya ce ni kuma ba zai yiwu na shige gaban wanda Manzon Allah (SAW) yake fada a cikin hakkinsa ba cewa wanda yake so ya yi duba izuwa kirjin Ibrahimu Khalilullahi to ya yi duba izuwa kirjin Abubakar Assidiku, sai Abubakar (RTA) ya ce ni ma ba zai yiwu ba na fara shige wa gaban Wanda na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa wanda ya me so ya yi duba izuwa Adamu ko izuwa Yusufu da kyansa ko izuwa Musa da sallarsa, ko izuwa Isa da gudun dukiyarsa ko izuwa Muhammadu da dabi'oinsa to ya yi duba izuwa Aliyu. Sai Aliyu (RTA) ya ce ni ma ba zai yiwu ba na shige gaban Wanda na ji Manzon Allah (SAW) yake cewa a cikin hakkinsa, idan talikai suka hadu a cikin cikin Alkiyama ranar tabewa da nadama, sai mai kira ya yi kira daga katarnin Ubangiji mabuwayi da daukaka, ya Abubkar ka shiga Aljanna kai da wadanda suke kaunarka, sai Abubakar (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban Wanda na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ranar yakin Hunainu da Kaibara hakika an kawo masa hadiyar dabino da nono cewa wannan hadiya ce (kyautar ce) daga mai Neman runjaye (nasara) izuwa Aliyu dan Abu Dalibi. Sai Aliyu ya ce ni kan ba zan shige gaban wanda Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba ya Abubakar kai ne idona, sai Abubakar (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda Manzon Allah (SAW) yake cewa a cikin hakkinsa ba, Aliyu zai zo akan abin nawa daga abin hawan gidan Aljanna sai mai kira ya yi kira ya Muhammadu Kannada Duba kyakkyawa a duniya kuma kana da dan uwa kyakkyawa, amma Uba kyakkyawa shi ne Ibrahimu Badadi, amma dan uwanja shi ne Aliyu dan Abi Dalibi (RTA). Sai Aliyu (RTA) ya ce ni kan ba zan shige gaban mutumin da na ji Manzon Allah yana cewa a cikin hakkinsa ba idan Alkiyama ta kasance Riddiwanu ma'ajin gidan Aljanna zai zo da mabudin gidan Aljanna da kuma mabudin gidan wuta sai ya ce Ya Abubakar shigar da wanda kake so cikin Aljanna kuma ka shigar da Wanda kake so gidan wuta.

Post a Comment