Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.


   Sai Abubakar ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba. Hakika jibrilu (AS) ya zo min sai ya ce ya Muhammadu hakika Allah mabuwayin daukaka yana karanta maka gaisuwa kuma yana cewa ina kaunarka kuma ina kaunar Aliyu sai na yi sujjada don godiya. Kuma ina kaunar Hassan da Hussaini. Sai na yi sujjada domin godiya. 

Sai Aliyu (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba. Da za'a auna imanin Abubakar da mazauna kasa da ya runjaye su.

Sai Abubakar (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba. Hakika Aliyu zai zo ranar Alkiyama a tare da shi akwai matarsa da 'ya'yansa akan abin hawa na daga dabbobi, sai ma'abota alkiyama su dinga cewa wannan wane Annabi ne? Sai mai kira ya yi kira yana mai cewa, wannan shine masoyin Allah. Wannan shine Aliyu dan Abi Dalibi.

Sai shi kuma Aliyu (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban mutumin da naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba. Gobe ranar tashin (Alkiyama) ma'abota tashi za su ji ana cewa ka shiga ta ina ka ke so daga kofofin shiga (Aljanna) guda takwas ya kai Assidiku mai girma.

Sai Abubakar (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba. A tsakanin katanga ta da katangar Ibrahimu akwai katangar Aliyu dan Abi Dalibi.

Sai Aliyu (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda naji Manzon Allah (SAW) yana cewa akan hakkinsa hakika mazauna sama daga Karubawa da Rauhanai da Mala'iku madaukaka wallahi suna dubawa izuwa Abubakar a kowa ce rana. 

Sai Abubakar (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda naji Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin hakkinsa ba, da hakkinka Ahlulbaitinsa suna ciyar da abinci tare da suna kaunarsa (ga) muskinai da marayu da kamamme. 

Sai Aliyu (RTA) ya ce ni kam ba zan shige gaban wanda na ji Allah (SWT) yana cewa a cikin hakkinsa wanda ya zo da gaskiya kuma ya gasgata da ita to wadannan su ne masu tsoran Allah.

 Sai Jibrilu Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya sauko izuwa mai gaskiya amintaccen Ubangijin talikai a cikin wannan lokacin sai ya ce ya Muhammadu madaukaki mai girma yana karanta gaisuwarsa a gare ka yana cewa da kai hakika Mala'ikun sammai bakwai suna yin duba a wannan lokacin izuwa Abubakar Assidiku da kuma Aliyu dan Abi Dalibi suna sauraran abin da ke gudana a tsakaninsu na daga kyakkyawan ladabi da kyakkyawan jawabi a junansu,
Ka tashi izuwa gare su ka zama kai ne ukunsu, domin kuwa Ubangiji ya kewaye su da rahamarsa da kuma yaddasa, kuma ya kebance su da kyakkyawan ladabi da Musulinci da imani.


Sai Annabi (SAW) ya fito izuwa gare su sai kuwa ya same su kamar yadda Jibrilu ya ambata, sai ya subbaci fuskar ko wane dayan su, sai ya ce rantse da wanda rai na ya tabbata a hannunsa. Da dai za'a ce teku zata zama rawada bishiyoyi kuma su zama alkama, mazauna sama da kasa su kasance suna marubuta da sun gajiya a wajen rubuta falalarku da yawan ladanku.

(Ma'abocin rauratul faiki ne ya rawaito shi)


1 Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post