Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.


An karbo daga Abdullahi dan Magafalin (RTA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce ina tsoratar da ku Allah a cikin Sahabbaina ina tsoratar da ku Allah a cikin sahabbaina, kafa ku rika su karan bara a bayana, wanda ya so su saboda kaunata yake kaunar su, wanda da yake gaba da su (ya ke kin su) saboda yana kina ne, Wanda kuwa yake cutar su hakika ya cuce ni, wanda kuwa ya cuce ni to hakika cuci Allah, wanda kuma ya cuci Allah to ya kusanta ya kama shi.

(Tirmizi ne ya rawaito shi)

An karbo daga Anas Allah yakara yadda a gare shi, ya ce Annabi (SAW) ya ce hakika tabkina yana da kusuruwa guda hudu kusuruwa ta farko tana hannun Abubakar, kusuruwa ta biyu tana hannun Umar, kusuruwa ta uku tana hannun Usmanu, Kuusruwa ta hudu tana hannun Aliyu. Wanda yake kaunar Abubakar yake gaba Umar to Abubakar ba zai shigar da shi na. wanda yake kaunar Umar yake gaba da Abubakar to Umar ba zai shigar da shi ba. Wanda yake kaunar Usmanu yake gaba da Aliyu to Usmanu ba zai shigar da shi ba. Wanda yake kaunar Aliyu yake gaba da Usmanu to Aliyu ba zai shigar da shi ba. Wanda ya kyautata magana ga Abubakar to hakika ya tsayar da addini, wanda ya kyautata magana ga Umar to hakika ya bayyana hanya, Wanda ya kyautata magana ga Usmanu to hakika ya haskaka da hasken Ubangijin Talikai, Wanda ya kyautata magana ga Aliyu to hakika ya yi riko da igiya mai karfi, Wanda kuwa ya kyautata magana ga Sahabbaina to hakika shi mumini ne, wanda ya muna na magana ga Sahabbaina to hakika shi munafiki ne.

(Manakibi ahahlulbaitinnabiyi (SAW))

Post a Comment

Previous Post Next Post