Bisimillahir rahmanur rahim da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Sahabban manzon Allah (S.A.W) wadansu bayin Allah (S.W.T) da ya fifita su a cikin wannan al'ummar babu wani musulmi da zai ta ba kamo kafar sahabi ko ya hada kafa dashi a cikin daraja, ko mai kokarinsa a cikin wannan addinin matukar da shi ba sahabi ba ne, haka zalika kuma shima sahabi ba zai taba kamar kafar annabi Muhammad (S.A.W) ba bare ma ya hada kafa dashi a wajan daraja.
Sai dai hakika Ubangiji madaukaki ya fifita darajojjin wadansu sahabban a kan 'yan uwansu sahabbai, kamar yadda ya fifita wasu annabawan akan 'yan uwansu annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su baki daya.
Mafi darajar Sahabbai a wajen ahlussunna da jama'a sune
• Abubakar
• Umar
Allah yakara yadda a gare su. Amma kuma an samu sabani akan
• Aliyu
• Usmanu
Allah yakara yadda a gare su baki daya. Wadansu sun fifita ALIYU akan USMANU, wadansu kuma sun fifita USMANU akan ALIYU. Amma kuma Imamu Malik ya ta ce, yace "ba za a fifita da a tsakanin USMANU da ALIYU ba" Allah yakara yadda a gare su. Amma yawanci malamai sun gabata da USMANU akan ALIYU (R.T.A).
Abu Mansuru Albagdadiyi yace "abokanmu su hudu akan cewa Khalifofin Manzon Allah (S.A.W) sune mafiya daraja a cikin sahabbansa (S.A.W) Sannan sai mutane shida cikwan mutane goman da aka yiwa bushara sa aljanna. Wannan sahabbai guda shida sune
• Dalhat
• Zubair
• Sa'adu
• Sa'idu
• Abdurrahman
• Ubaidata
Wadannan sune Sahabbai guda shida, idan ka hada da Khalifofinsa guda hudu sun zama guda goma kenan waddan da Allah yayi musu bushara da Aljanna a kan harshen Manzon Allah (S.A.W).

Post a Comment