Abin da annabi (S.A.W) yake nufi da karninsa wadanda sukayi zamani da shi. Kuma suka ganshi su kayi imani da shi,
Karni na biyu kuma sune tabi'ai wadanda suka ga sahabbai su kayi imani da manzon Allah (S.A.W).
Karni na uku sune tabi'ittabi'ina, wato sune suka ga sahabban manzon Allah (S.A.W).To wadandan sune zabbabun wannan al'ummar kuma mafi alkairinta Wanda manzon Allah (S.A.W) ya tabbatar da hakan a hadisansa. Duk wani tabi'i zai yi wa addini ba zai kama darajar takalmin sahabi ba daga cikin sahabban manzon Allah (S.A.W).
Wanene sahabi?
Sahabi shine Wanda yayi zamani daya da manzon Allah (S.A.W) ya ganshi da idanunsa kuma ya bada gaskiya da shi har ya mutu akan imani ko da da kiftawar da bisimillah ne.
Menene Karni?
Shine rayuwar jama'a ma'abota zamani daya. Akan wani abu da suka hadu akan sa a wannan zamanin. Anyi sabani akan gwargwadon Karni, ance daga shekara guma (10) izuwa shekara dari da ashirin (120).
Amma abinda ake nufi da karnin annabi (S.A.W) a cikin wannan hadisin sune sahabban manzon Allah (S.A.W) karshen kuwa wanda ya mutu daga cikin Sahabban annabi (S.A.W) babu wani sabani shine : Abu Du-failin Aumiru dan Wasilata Allaihi (R.T.A) shi wannan ya mutune a cikin shekara ta dari (100) abisa ingantacciyar magana.
ADADIN YAWAN SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W).
Babu wanda yasan adadin yawan sahabban manzon Allah (S.A.W) sai Allah madaukakin sarki. Saboda yawan wadanda suka musulinta. Daga ranar aka aiko izuwa ranar mutuwarsa (S.A.W) hakika an rawaito cewa an karbi ran manzon Allah (S.A.W) a yayin da sahabbansa suka kai su dubu dari da dubu dari ashirin da hudu (124,000), na karshen mutuwarsu shine Abu Du-failin Aumiru dan Wasilata Allaihi allah ya kara yadda a gare su.
thanks for share this one
ReplyDeletePost a Comment