Bismillahir rahmanur rahim. Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Malaman farko na ahlussunna da na karshensu sun hadu kan cewa sahabban manzon Allah (S.A.W) sune mafi alkarin wannan al'ummar. Sannan tabi'ai Sannan tabi'ittabi'ina kamar yadda yazo cikin hadisai kamar haka:-
• An karbo daga Imrana dan Hussain (R.T.A) yace:
Annabi Muhammad (S.A.W) yace mafi alkairin al'ummata ( wadanda sukayi zamani da ni ) Sahabbai. Sannan kuma wadanda suka biyu bayan su (tabi'ai) sai Imrana yace , ban sani ba a bayan karni na biyu ya ambata ko na uku ne? Sannan hakika a bayan ku za a samu wadansu jama'ar da za su dinga bayar da shaida tun gaban ba a nemi su zo su bayar da shaidar ba kuma za su dinga yin ha'inci da baza a amince musu ba, kuma za su dinga yin alkawari ba sa cikawa, kuma za su dinga yin kiba (kaurin jiki).
Bukari da Muslim da tirmizi da nisha'i ne suka rawaito.
•An karbo daga abdullahi (R.T.A) yace:
Annabi Muhammad (S.A.W) yace mafi alkairin mutane karni na, Sannan na bayan su, Sannan wadanda suke biye da su, Sannan sai wata jama'a su kuma zo, wandada shaidar dayan su take riga rantsuwar su kuma rantsuwar su tariga shaidar su.
Bukari da Muslim da tirmizi suka rawaito.
•Daga Nana Aisha Allah ya kara mata yadda tace an tambayi manzon Allah (S.A.W) cewa wadda na mutane ne fiyayyu sai yace: Karni na da nake cikinsa, Sannan na biyun sa, Sannan na ukun sa.
Muslim ne ya rawaito.
Good job 👌 keep it up 👍
ReplyDeletePost a Comment