Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
An karbo daga Abu Sa'idul-Khudri (RTA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce, kada ku zafi sahabbaina, na rantse da Wanda rai na yake hannunsa, da dayanku zai ciyar da misalin dutsen Uhudu na zinare da ba zai kai mudu dayansu ba kai ko rabinsa ma.
(Tirmizi ne ya rawaito shi)
Annabi (SAW) ya ce, hakika Allah ya zabe ni, kuma ya zaba min sahabbai, kuma ya sanya min wazirai daga cikinsu da mataimaka da surukai, saboda haka tsinuwar Allah da Mala'iku da mutane gaba dayansu ta tabbata a gare shi, kuma ranar Alkiyama Allah ba zai karbi aikinsa na farilla ko na nafila ba.
(Haisami da dabarani ne suka rawaito shi)
An karbo daga Anas dan Malik (RTA) ya ce mutane daga sahabban Manzon Allah (SAW) sun ce hakika mu ana zagin mu, sai Manzon Allah (SAW) ya ce wanda ya zagi Sahabbai na tsinuwar Allah da Mala'ikunsa da mutane gaba dayansu ta tabbata a gare su.
An karbo daga Anas (RTA) ya ce Manzo Allah (SAW) ya ce hakika Allah ya zabe ni kuma ya zaba min sahabbaina, kuma ya sanya min abokai da 'yan uwa da surukai, to da sannu wandasu jama'a za su zo a bayansu za su dinga aibata su kuma su dinga tauye darajojinsu (to idan ku ka yi zamani daya da su) kada ku ci abinci tare da su, kafa Ku sha ruwa tare da su, kada muyi musu sallah, kuma kafa muyi sallah tare da su.
(Muntakhabu Kanzul Ummal)
An karbo daga dan mas'udin (RTA) ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce idan aka ambaci taurari ku kame, idan aka ambaci kaddara ku kame.
(Dabarani ne ya rawaito shi)
MAI ZAGIN KHALIFOFIN ANNABI BA ZAI CIKA DA IMANI BA.
Ya zama wajibi akan ko wane musulmi mai imani idan ya ji ana ambaton daya daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) ya kame bakinsa da barin abin da ya gudana a tsakanin su, domin kuwa su sahabbai ba Annawa ba ne, su sahabbai mahafuzai ne ba ma'asumai ba ne, saboda haka idan anga sahabi ya aikata wani abu da ya sabawa shari'a to kamata ya yi a nema masa gafara bai kamata a la'ance shi ba.
Akwai wani sahabi ya kance yana shan giya har sai da Manzon Allah (SAW) ya sa aka yi masa haddin bulala har sai uku. Sai wadansu daga cikin sahabbai suka dinga la'antarsa, sai Manzon Allah (SAW) ya ce ku dai na la'antarsa domin yana kaunar Allah da Manzonsa.
Zagin sahabbai ko yin gaba da su kamar wani fito na fito da Ubangiji (SWT) domin kuwa babu wanda yake kokwanto akan cewa sahabban Manzon Allah (SAW) sune waliyyan Allah.
Manzo Allah (SAW) ya ce Allah (SWT) ya ce wanda ya ke gaba da wakiyyai na to hakika ina sanar da shi yaki.
(Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi)
Saboda haka ne ake jin tsoron idan mutum yana tare da masu zagin sahabbai ko gaba da su to ba zai cika da imani ba, kamar yadda ya zo a cikin hadisi.
An karbo daga Abdurrahman Almuharabiyu (RTA) ya ce, an halarci mutuwa wani mutum, sai aka ce da shi ce ne (LA'ILAHA ILLALLAHU) sai ya ce ba zai iya fada ba, saboda na kasance nayi abota da wadansu mutane da suke umarni na akan na zagi Abubakar da Umar, Allah ya kara yadda a gare su.
(Ibin Askira ne ya rawaito shi)
KARSHEN LITTAFIN
KHALIFOFIN ANNABI MUHAMMADU (SAW)
thanks for share this one
ReplyDeletePost a Comment