Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah mai rahama mai jin kai.


  Ayoyin Alkur'ani mai girma sunyi furici da matsayin sahabbai manzon Allah (S.A.W) da irin kaunar da suke yi wa junansu da kuma tsanantawa da suke yi akan kafirai makiyan allah da manzon sa da jajircewar su akan taimakawa manzon Allah (S.A.W) akan har sai ya isar da sakonsa.

Allah madaukaki yana cewa:- 


Fassarar wannan ayar:-

MUHAMMADU MANZON ALLAH NE. WADANDA SUKE TARE SHI (SAHABBAI) MASU TSANANIN TSANANTAWA NE A KAN KAFIRAI. MASU TAUSASAWA NE A TSAKANIN SU. KANA IYA GANIN SU MASU YAWAN RUKU'U MASU YAWAN SUJJADA SUNA MASU NEMAN FALALA DAGA UBANGIJI ALLAH DA KUMA YARDA. KAMANNINSU YANA CIKIN FUSKOKIN SU NA DAGA KUFAN SUJJADA. WANNAN SHINE SIFFARSU A CIKIN ATTAURA. KUMA SUFFARSU, A CIKIN INJILA ITA CE KAMAR TSIRON SHUKA WADDA YA FITAR DA RESHENSA,SA'AN NAN YA KARFAFA SHI, YAYI KAURI, SA'AN NAN YA DAIDAITA SHI AKAN KAFAFUNSA. YANA BAYAR DA SHAWARA GA MASU SHUKAR DOMIN (ALLAH) YA FUSATAR DA KAFIRAI GAME DA SU. KUMA ALLAH YAYI WA'ADI GA WADANDA SUKAYI IMANI, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN KWARAI, DAGA CIKIN SU,  DA GAFARA DA IJIRA MAI GIRMA.

1 Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post